Me ka ke nema?


Shafin Farko

Majalisar Tarayya - Amurka



Zauren Majalisar Amurka   Hoto:Aljazeera


Gabatarwa

Kongires ko Kwangires, wato Congress kenan a Turance. Ita ce Majalisar Tarayyar Amurka wadda aka kafa bisa umarnin kundin tsarin mulkin Amurka na shekarar 1789, shekaru ɗari biyu da talatin da biyu (232; 1789 – 2021) kenan da suka shuɗe. Majalisa mai tagwayen zauruka ko rassa biyu; Ƙaramar Majalisa (Lower Chamber), wadda ita ce Majalisar Wakilai (House of Representatives) da kuma Babbar Majalisa (Upper Chamber) wadda kuma ita ce Majalisar Dattawa (House of Senate).

Kundin Tsarin Mulkin Amurka, sake ba ƙaidi, ya ɗora alhakin yin dokoki, ayyana yaƙi, 'yancin tabbatarwa ko yin fatali da wasu naɗe-naɗen shugaban ƙasa masu tarin yawa da kuma cikakken ikon gudanar da bincike a kan wannan majalisa.

Ƙarfin Iko

An darajta ƙarfin-faɗa-a-ji da jama'a suke da shi ta hannun wakilan da suka zaɓa a tanadin farko (Article I) na Kudin Tsarin Mulkin Amurka wanda ya kafa Majalisar Tarayyar Amurka mai tagwayen zauruka. Saka wannan majalisa a farkon kudin tsarin mulki ya tabbatar da darajarta a matsayin reshen farko (First Branch) na gwamnatin Tarayyar Amurka. Kenan, Majalisar Tarayyar Amurka, ita ce sama duk wata hukuma a Amurka ciki kuma har da fadar shugaban ƙasa.

Kundin Tsarin Mulkin ya damƙa wa majalisar ɗawainiyoyin tsara rassan zaɓaɓɓu (Executives) da kuma shari'a (Judiciary), tara haraji, ayyana yaƙi, da kuma yin dokokin da suka dace a lokacin da ya dace domin gudanar da mulki. Duk da cewa shugaban ƙasa yana iya hawa kujerar na ƙi game da wasu dokokin majalisa, to ita kuma majalisa tana da ƙarfin janye waccar dama ta shugaban ƙasa ta hanyar samun ƙuri'u mafiya rinjaye da biyu cikin uku da dukkan majalisu biyun suka kaɗa domin yin haka. Tabbatar da wasu naɗe-naɗe da suka shafi ɓangaren zaɓaɓɓu da shari'a tare kuma da tantance yarjeniyoyin ƙasa-da-ƙasa duk yana wuyan majalisa.

Kundin Tsarin Mulkin Amurka a kashinsa na farko ya ce: "Duk wani ƙarfi na yin doka wanda ke cikin wannan kundi a ɗora shi a kan Majalisar (Congress) Tarayyar Amurka, wadda ke da Majalisar Dattawa da ta Wakilai". Mai karatu, kafa ji yadda lamarin yake. Amma, a juri ziyaratar wannan shafi, za a cigaba da sabunta rubutun.

Manazarta

Library of Congress (Babu shekara). About the Congress. An ciro a 2021, daga https://www.congress.gov/about

The White House (Babu Shekara). The Legislative Branch. An ciro a 2021, daga https://obamawhitehouse.archives.gov/1600/legislative-branch

United States Senate (2019). Class I - Senators Whose Term of Services Expire in 2025. An ciro a 2021, daga https://www.senate.gov/


Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub